Gwamnan Jihar Barno da ke Najeriya Babagana Umara Zulum ya gabatar da bukatu guda 6 ga tawagar gwamnatin tarayya wadda ta kunshi sake hayar sojojin haya daga kasashen ketare domin murkushe mayakan boko haram da suka addabi jihar sa.
Zulum ya gabatar da bukatun ne lokacin da ya karbi tawagar gwamnatin a karkashin shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan wadanda suka je jajantawa jama’a kan kisan gillar da mayakan boko haram suka yiwa wasu manoma.
Idan dai ba a manta ba lokacin mulkin shugaba Goodluck Jonathan, Najeriya ta yi hayar wadannan sojojin haya daga Afirka ta kudu wadanda aka dinga amfani da su ana yakar boko haram.
Daga cikin bukatun Zulum akwai dibar matasan yankin cikin aikin soji da sauran hukumomin tsaro da karfafa hadin kai tsakanin Najeriya da hukumomin Chadi da Kamaru da Nijar domin karkade lungunar da mayakan suke makalewa, sannan kuma da bai wa sojoji da ‘yan sandan Najeriya motoci masu sulke da ingantattun kayan aiki domin shawo kan matsalar.
Gwamnan ya kuma bukaci taimakon gwamnati wajen kwaso ‘yan Jihar da suka nemi mafaka a kasashen Nijar da Kamaru, kana da sake gina hanyoyin Jihar da suka lalace sakamakon rikicin boko haram da aka kwashe shekaru 11 ana yi.