Biden ya gabatar da wannan jawabi ne a mahaifarsa ta Wilmington a gaban dimbim magoya bayansa, ga kadan daga abin da ya ke cewa.
Jawabin nasarar da Biden ya gabatar ya biyo bayan gwabzawa mai zafi da suka yi da shugaban Amurka mai ci, Donald Trump a takarar shugabancin kasar, a daidai lokacin da annobar coronavirus ke ta’azzara a kasar.
Biden wanda ya yi alkawarin kawo hadin kai a kasar ya yi kira ga, magoya bayan Trump da su kwantar da hankulansu, don su ba abokan gaba bane, ‘yan Amurka ne su.
Daga nan sai ya sha alwashin maido da kimar Amurka a idon duniya.