Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sabon shugaban karamar hukumar Tarauni Honourable Abubakar Zakari Muhammad Habu P.A yasha alwashin hada kai da Mataimakinsa dukkanin kansiloli wajen aiki dan samun dai daito da kyakykyawan wakilincin karamar hukumar a kowane mataki,

A jaqabinsa yayin bikin rantsar da mataimakinsa da kansiloli 10 na karamar hukumar da akayi ranar laraba a sakatariyyar karamar hukumar Habu P.A yace lokaci yayi da zaa samar da yanayi da alummar Tarauni zasu ci gajiyar zabin da sukayi kamar yadda ya kamata dan haka mu a shirya muke dan hada kai da duk masu ruwa da tsaki na jammiyya da dukkanin alummar da suke son cigaban karamar hukumar dan aiki tare,

Sabon shugaban karamar hukumar ya kara da cewa ku sani yanzu kowa yana da hakki akammu da dan jamiyyarmu da wanda ba dan jamiyyarmu bane matukar dan karamar hukumar mu ne saboda haka akwai bukatar hada kai dan mu sauke nauyin da yake kammu,

Daganan sai ya bukaci maikatan karamar hukumar dasu bawa sabbin kansilolin cikakken hadin kai dan gudanar da aiki kamar yadda ya kamata, tare da jan kunnen ko wane bangare na aiki daya kiyaye dokokin aiki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada,

Kafin zabin nasa a matsayin shugaban karamar hukuma Abubakar Zakari Muhammad Habu P.A YA wakilin karamar hukumar Tarauni a Majalisar dokokin jihar, kafin daga bisani a nafashi Babban Sakataren a hukumar bada tallafin karatu ta jihar kano.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *