Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kwantaragin dan wasan baya na Brazil David Luiz da Arsenal za ta kawo ƙarshe a ranar 30 ga Yuni amma wakilin ɗan wasan mai shekara 33 ya ce suna fatan sasantawa kan makomarsa a ƙarshen mako. (Talksport)

Luiz na son a tsawaita kwantaragin tsawon shekara biyu amma kuma Arsenal na son ƙara masa watanni 12 ne kawai. (Mail)

Chelsea na son sayar da dan wasan Faransa N’Golo Kante, mai shekara 29, domin ta samu kuɗaɗen da za ta karɓo ɗan wasan Jamus Timo Werner daga RB Leipzig. Times

Chelsea na fatan karɓo dan wasan tsakiya na Bayer Leverkusen Kai Havertz zai sa Bayern Munich da Real Madrid haƙura da ɗan wasan na Jamus mai shekara 21. (Express)

Inter Milan na tattaunawa da Manchester United domin ci gaba da ajiye ɗan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, a matsayin aro har zuwa baɗi. (Sky Italia, via Mirror)

Arsenal da Manchester United dukkaninsu suna son dan wasan Roma Cengiz Under, inda darajar ɗan wasan mai shekara 22 ta kai £27m. (Corriere dello Sport, via Mail)

Barcelona na son riƙe Messi har 2023, Ronaldo na son komawa MLS
Timo Werner: Chelsea ta bai wa dan kwallon RB Leipzig yarjejeniyar shekara biyar

Bayern Munich ta amince ɗan wasan Brazil Philippe Coutinho ya ci gaba da murza leda a kulub ɗin da ta karbo aro daga Barcelona inda yarjejeniyarsu za ta kawo karshe 30 ga Yuni.

Bayern na son ɗan wasan mai shekara 28 ya ci gaba da buga mata gasar zakarun Turai a Agusta. (Sky Germany, via Mirror)

Everton za ta rasa dan wasan da take farauta Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, daga Lille yayin da ɗan wasan baya na Brazil ke shirin komawa Napoli.(Footmercato, via Mail)

Everton na son ɗauko ɗan wasan Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 23 daga kulub din Beijing Guoan. (Guardian)

Ɗan wasan tsakiya na Brazil Fernandinho, wanda kwangilarsa da Manchester Cityza ta kawo kare har zuwa 2021, ya ce yana son ya yi ritaya a ƙasarsa. (Gazeta do Povo

Manchester Evening
News

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *