Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wakili karamar hukumar Birnin Kano a majalisar wakilai ta kasa Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada yace zaben kananan hukumomi da ake cewa an.gudanar a jahar Kano kwanakin baya da cewa wulakanta jam’iyyarsu ta APC ne daga jagororinta na jahar Kano.
dan majalisar ya bayyana hakane a zantawarsa da wata kafar watsa labarai a Kano inda yace zaben burum burum ne da wasan kwaikwayone da Gwamnatin Kano tayi amfani da tsabar kudi Naira Biliyan Biyu domin shirya shi.

Sha’aban Sharada Wanda tun bayan zaben fidda gwanin cikin jam’iyyar APC na fidda na takarar shugabancin kananan hukumomi da kansiloli ya kalubalanci yanda aka gudanarda zaben yace basa tareda yadda akayi zaben na kananan hukumom.i Dama shugaban jam’iyyar na Jihar Kano ya fito karara ya bayyanawa Duniya cewa rubutawa zasuyi.

dan majalisar na tarayya mai wakiltar Birnin Kano yace wannan nema ya sa jam’iyyar hamayya ta PDP a kano.ta kaurace wa shiga zaben da akace anyi.

Yace bangaren magoya bayansu da suka nemi. shiga zaben fidda gwanin a karamar hukumar Birnin Kano an hanasu duk wata dama da karfin tsiya, wanda da an tsaya an gudanarda zaben cikin gida bisa adalci da ra’ayin jama’a sunada yakinin samun nasara.
Sha’aban yace amma a karamar hukumar Birnin Kano an dauko mafi karancin goyon bayan al’umma da yan lele an kakabasu ance sune yan takara da akace sunci zaben,wannan abin.kunyane da tozarta jam’iyyar APC.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *