Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumomi a Najeriya sun ba wa rundunar ƴan sandan ƙasar damar amfani da duk wata hanya ta tsaurara matakan tsaro a kokarin kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke a wasu sassan ƙasar.

An samu rikici musamman a biranen Legas da Abuja, a dalilin zanga-zangar kin jinin rundunar ƴan sanda da ke yaƙi da fashi da makami da a kafi sani da SARS, wadda ta yi sanadin mutuwar a kalla mutun 69.

Rahotanni sun ce an saka dokar hana fita a wasu yankunan jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, da kuma birnin Jos na jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, inda a ka samu rahotannin fasa rumbunan ajiyar abinci na gwamnati a ka kuma wawashe su.

Bbc ta ruwaito Sufeta-Janar na ƴan sandan Najeriya Muhammed Adamu ya ce ƴan ta’adda sun ɓadda kama da sunan masu zanga-zanga wurin aikata miyagun ayyuka a sassan ƙasar da dama.

Lamarin ya fi ƙamari a cibiyar kasuwancin ƙasar wato Legas, inda ganau su ka shaida cewa jami’an tsaro sun harbe masu zanga-zangar da a ka yiwa lakabi da #ENDSARS

 

A ranar Asabar gwamnatin Jihar Kaduna ta saka dokar hana fita a wasu yankuna na ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu da kuma Chukun ta tsawon awa 24.

Dokar za ta yi aiki ne a unguwannin Barnawa da Kakuri da Television, waɗanda ke Kaduna ta Kudu.

Sai kuma Maraban Rido da Sabon Tasha da Narayi da Unguwan Romi da ke Chukun.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki ne nan take.

Mista Aruwan ya yi kira ga mazauna jihar da su guji tayar da tarzoma da kauce wa faɗawa tarkon masu tayar da husuma.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *