
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce, tana gudanar da bincike domin gano musabbabin mace-macen da ake fama da su a jihar Kano, inda a cikin kwanaki biyu, aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 150 a jihar, matuwar da wasu ke danganta wa da cutar COVID-19.
Shugaban Gudanarwar Kwamitin Shugaban Kasa da ke Yaki da COVID-19 a Najeriya, Dr. Sani Aliyu, ya sanar da haka a birnin Abuja.
Tuni kwamitin ya tashi tawagar mutun 17 zuwa Kano don gudanar da bincike kan lamarin a jihar.
Rahotanni sun ce, tsakanin Juma’a zuwa Asabar da suka gabata, an gudanar da jana’izar gawarwaki fiye da 150 a makabartu uku kacal da ke Kano.
Lamarin ya jefa tsoro a zukatan al’umma da ke zargin cewa, wata sabuwar cuta ce take lakume rayuka sannu a hankali a jihar.
Majiyarmu ta zanta da masu aikin hakar kaburbura, inda suka shaida masa cewa, lallai yawan mace-macen ya tayar musu da hankali, domin kuwa raban da su ga irin wannan mutuwar, tun lokacin da aka kaddamar da harin bam a Masallacin Juma’ar Kofar Gidan Sarkin Kano.