Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Aedes aegypti mosquitoesASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Hukumomi a jihar Florida ta Amurka sun amince da sakin wani cincirindon sauro miliyan 750 da aka jirkita ƙwayoyin halittarsu.

Burin yin hakan shi ne rage adadin sauron da ke ɗauke da cutuka irin su dengue ko kuma ƙwayar cutar Zika.

An shafe shekaru ana tafka muhawara kan matakin gwajin irin wannan nau’in na sauron duk da masana muhalli sun bayyana cewa akwai yiwuwar wani mummunan sakamako zai iya biyowa baya.

Masana sun yi gargaɗin cewa wannan gwajin da za a yi zai iya kawo matsala ga doron ƙasa, ta hanyar samar da sauron da ba su jin magani.

Sai dai kamfanin da ke wannan aikin ya ce babu wani hatsari ga bil adama ko kuma muhalli.

Yunƙurin da ake yi na sakin sauron a 2021 a Florida na zuwa ne watanni kaɗan bayan hukumomin tarayyar ƙasar sun amince da sauron da aka inganta.

A watan Mayu ne hukumar kula da muhalli ta Amurka ta bayar da dama ga kamfanin Oxitec mallakar Birtaniya damar samar da wani nau’in sauro irin samfarin Aedes aegypti kuma namiji.

Sauro samfarin Aedes aegypti sun yi fice wurin baza manyan cutuka ga bil adama da suka hada da dengue da Zika da chikungunya da ciwon shawara.

A biologist in Brazil releases Oxitec to combat a Zika outbreakASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Ta macen sauro ne kaɗai ke cizon ɗan adam sakamakon suna buƙatar jini domin su yi ƙwai. Shirin da ake da shi a halin yanzu shi ne na a saki namijin sauro wanda zai haɗu da matan sauro da ke cikin duniya inda ake sa ran za su samar da wani nau’i na daban na sauro.

Namijin sauro na ɗauke da wani sinadarin protein da zai kashe duk wata macen sauro kafin ta riƙa ta fara cizo.

Mazan waɗanda kawai suke rayuwa ta hanyar tsotsar ruwan itatuwa za su ci gaba da rayuwa domin samar da irin waɗannan ƙwayoyin halittar da aka inganta.

Nan da wani lokaci mai zuwa, shirin da ake da shi, shi ne rage yawan sauro samfarin Aedes aegypti a yankin inda hakan zai rage yaɗa cutuka ga mutane.

Bbc ta ruwaito cewa akwai mutane da dama da suka caccaki wannan yunƙuri inda kusan mutum 240,000 suka sa hannu a takardar koke a shafin Change.org inda suke zargin kamfanin Oxitech da amfani da Amurka a matsayin wurin gwajin wannan sauron.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *