Gwamnatin Jihar Legas ta nuna matukar damuwa game da yadda ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba da kuma karuwar adadin masu yin talla a manyan titunan mota, Daily Trust ta ruwaito.
A dalilin haka, ta umarci hukumar tsabtace muhalli ta jihar (LAGESC) da ta kori ‘yan tallan da ke yawo a kan manyan hanyoyin jihar.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa, Mista Tunji Bello, ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai LAGESC.
Mista Bello ya ce, “Akwai bukatar jami’an LAGESC su tabbatar da cewa duk manyan hanyoyi a cikin jihar sun kubuta daga duk wata matsala ta muhalli da keta doka domin tabbatar da tsaftar muhalli gaba daya.”
Bello ya lura da karuwar masu talla a wasu manyan tituna a tsibirin Victoria da kuma Mainland, inda ya umurci jami’an LAGESC da su shige gaba don tabbatar da cikakken tsafta.
A cewarsa, hanyoyin ba an yi su don cinikayya bane, kuma ya kamata mutane su shiga kasuwannin da jihar ta amince da su don gudanar da ayyukan kasuwanci na doka.
Sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da taimako da goyon baya da suka dace kamar karfafa ma’aikata, inshora da ingantaccen aiki yadda ya kamata.
Kwamishina, saboda haka, ya gargadi jami’an da su guji duk wani nau’i na ayyukan rashin tsafta, yana mai gargadin cewa duk wani jami’in da aka samu yana da laifi za a hukunta shi yadda ya dace.
Tun da farko a jawabin maraba, LAGESC Corps Marshal, CP Akinpelu Gbemisola (Rtd), ta ce ziyarar za ta “kara wa ma’aikata kwarin gwiwa kuma ta sa su ji cewa su ma suna da mahimmanci wajen ci gaban wannan gwamnati.”