Laakari da yadda rikicin boko haram ke sauyawa daga wannan ziwa wancan da yadda yakin yaki ci yaki cinyewa tsohon hafsan Sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai (mai murabus), a ranar Alhamis ya ce da yiwuwan wannan rikicin na Boko Haram ta cigaba har tsawon shekaru ashirin masu zuwa.
Ya ce da dadewa, yan ta’addan sun canza akidun mutane, kuma hakan zai sa kawo karshen yaki abu mai matukar wuya.
Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya gurfana gaban kwamitin harkokin wajen Najeriya na majalisar dattawa domin tantanceshi matsayin Ambasada.
Tsohon Sojan ya ce duk da cewa Sojojin Najeriya na samun hadin kai daga kasashe makwabta irinsu Kamaru, Chadi da Nijar, kuma ana samun nasara, amma karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen yakin ba.
Buratai ya ce akwai matsalolin siyasa da tattalin arziki da ya kamata a magance tukunna, saboda yawancin garuruwan Arewacin Najeriya na da karancin abubuwan more rayuwa.
“Sojojinmu na hada kai da Sojin Chadi da Kamaru. Mun samu nasarori. Amma yan ta’addan sun ratsa zukatan al’umma,” yace.
“Jihata Borno ce hedkwatar inda akayi masifar ratsa zukatan mutane sosai. Ba abinda zaku iya cire dare daya bane.”
“Sojoji kadai ba zasu iya magance matsalan ba. Akwai matsalolin tattalin arziki da ya kamata a magance. Ya kamata akwai kayan more rayuwa, amma babu.”