Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga-Salisu Musa Jegus

Zlantan

Daraktan wasannin AC Milan Paolo Maldini ya ce za a sabunta kwantaragin Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, ba tare da wani sharadi ba idan suka cancanci shiga gasar Zakarun Turai. (Mail)

Kocin Roma Paulo Fonseca yana son aron Chris Smalling, dan wasan Manchester United dan kasar Ingila mai shekara 30 da kuma dan wasan Arsenal dan kasar Armenia Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 31. (Sky Sports)

Manchester United na shirin sayen dan wasan Wolverhampton Wanderers da Portugal Diogo Jota, mai shekara 23 a kan £50m a bazara. (Express)
Wolves da Burnley na shirin fafatawa da Sheffield United wajen sayo dan wasan Leeds dan kasar Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 24.(Daily Star)
An yi amannar cewa kocin Paris St-Germain Thomas Tuchel yana tattaunawa da Bayern Munich da zummar komawa kungiyar ta kasar Jamus. (90 Min)

Masu zabar dan kwallon da za a saya na Liverpool sun je kallon ledar da dan kwallon Brighton Ben White, mai shekara 22, wanda Leeds ta yi aronsa ya murza. (The Athletic, via Inside Futbol)

Barcelona na daf da kammala sayen Hugo Guillamon, mai shekara, 20, wanda ke rukunin ‘yan wasan da ke kan benchi mai suna Mestalla na kungiyar Valencia. (Sport)

Crystal Palace na sanya ido kan dan wasan Eintracht Frankfurt Filip Kostic domin ya maye gurbin dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 27 a kan £10m. Liverpool ta taba yin zawarcin dan kasar ta Serbia, mai shekara 27. (HITC, via Sun)

Aston Villa da West Ham na duba yiwuwar sayo dan wasan GillinghamJack Tucker, mai shekara 20. (Birmingham Mail)

Rangers na sha’awar sayo dan wasan West Brom Rayhaan Tulloch. Kwantaragin dan wasan mai shekara 19 zai kare a Hawthorns a kakar wasan da muke ciki. (Mirror)

Manchester City za su yi atisaye a filin wasan Atletico Madrid ranar Laraba da safe gabanin karawar da za su yi da Real a Bernabeu a daren ranar. A filin wasan na Wanda Metropolitano aka buga wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce. (AS)

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *