Daga -Kasim Gambo Kasim

Gwamnatin jahar kano tace zata kara wa’adin ranakun fita in har alumma suka yi biyayya ga tsare tsaren masana harkokin lafiya na Kare kai daga kamu da cutar corona.
Gwamnan kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hakan yayin da yake taro da shuwagabannin ‘yankasuwar jahar Kano kan bude kasuwannin a Africa house dake gidan gwamnatin Kano.
Ganduje yace” in har alumma musamman ‘yan kasuwa suka karbi dokokin Kare lafiya ta amfani da kyallen rufe fuska da wanke hannaye akai akai da bada tazara yayin gudanar da maamalarsu to gwamnatin zatayi duba kan Karin wa’adin”.
Ganduje, ya kuma jajantawa yan kasuwar na rife kasuwanin tsahon kwanaki sama da arba,in sakamakon cutar corona.
Gwamna Ganduje, yace zai hada hannu da gwnatin tarayya domin tallafawa yan kasuwar domin cigaba da farfado da harkokin kasuwanci afadin jahar nan.
Wakilin mu na ofishin gwamna Kassim Gambo kassim ya rawaito mana cewa, shuwagabannin daukacin kasuwannin jahar Kano sun yi alkawarin amfani da safar fuska da wanke hannaye tare da bada tazara yayin hadahadar kasuwannin nasu.