Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tun bayan da harkokin tsaro sukai sakwa sakwa sakamakon Hare

haren kungiyar Boko Haram a lokacin gwamnatin data shude inda aka dinga amfani babura wajen kai hare hare da kisan mutane a tsere bisa Babur a gurare daban daban a fadin jihar kano, a wancan lokaci ne gwamnati ta fitar da dokar hana hawa babur mutum biyu wato goyo,da nufi dakile hare hare kan babura.

Sai bayan da alamura sukayi sauki ne gwamnatin tayi shiru inda alummar suka cigaba da shaanin gabansu ciki harda goyon da a wancan lokacin aka hana,

A wannan lokacine ba zato ba tsammani sai gashi an fidda sanarwar cewa waccan doka ta hana goyo a babur ta dawo, sanarwar data fita ta bakin kakakin hukumar karota Nabulisi Kofar Naisa Sabanin inda sanarwar ta saba fita wato ta bakin hukumar yan sanda,

A tattaunawar sa da wakilinmu, kakakin hukumar kula da tituna da ababan hawa ta jihar kano Nabulisi Kofar Naisa yace ya zama wajibe a hana goyo a bayan babur lakari da yadda wasu ke yunkuri dawo da haya da babur tare da basaja wajen amfani da babura masu tsada suna fakewa wajen haya dasu abin da ka iya dawo da bara bana, inda yace hukumar ta karota ta gano yadda ake amfani da motobi da ireirensa wajen daukar mutane haya abin da Nabulisin yace kasan cewar karota hukuma daya daga cikin kwamitin tsaro na jiha bazasu lamunci haka ba,

Inda yace zasu hada kai da hukumomin kwamitin tsaro na jihar kano dan ganin dokar ta dore duk da cewa wasu na cewa dokar sarki ce wacce bata wuce kwana kadan,

Abin jira a gani shine duba da halin matsi da ake ciki ko za a sassautawa wadanda ke samun rage hanya sakamakon dokar kulle da halin da cutar corona ta jefa alumma na rashin kudin da zasu iya biyan kudin abin hawa ? Inda ake ganin mutane da dama na tattaki mai nisa ?

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *