Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ranar matan karkara ta duniya, rana ce da a ke maida hankali wajen haska fitila a kan matsalolin da suka addabi mata dake zaune a yankunan karkara.”

A bana an gudanar da bukin ne da taken, “Matan karkara da ‘yammata da suke kara jajircewa.” Majalisar Mata tana amfani da wannan dama wajen yin kira da a dauki matakan da zasu kai ga ba mata da ‘yammata damar cimma gurinsu na rayuwa.

Majalisar ta ce za a iya yin haka ne ta wajen ba matan damar da za su iya ci gaba a zamanin da ake fuskantar sauyin yanayi, su iya kara ci gaba a fannin harkoki noma da samun isasshen abinci da kuma albarkatun kasa, bisa la’akari da cewa, inda matan karakara suka fi karfi ke nan
Voa taruwaito cewa an fara kiyaye ranar matan karkara ta duniya ne a shekara ta 2018 bayanda Taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin doka mai lamba 62/136 da aka tsayar ranar 18 ga watan Disamba shekara ta 2007 wadda ta jadada muhimmancin gudamuwar da matan karkara suke badawa a harkokin noma da samar da abinci, da kuma yakar talauci.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, matan karkara suna bada gagarumar gudummuwa ga tattalin arzikin yankunan karakara da kuma kasashe masu tasowa har ma da kasashen da suka ci gaba. Bisa ga cewar Majalisar Dinkin Duniya, matan karkara suna bada gudummuwa ga ayyukan noma a gonaki, da kiwo, da sarafffa albarkatun gona, da girki da diban ruwan, da dai sauran ayyukan kula da iyali da suka hada da renon ‘yayansu da kula da marasa lafiya da kuma tsofaffi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *