Daga-Abubakar Sale Yakub

Sakamakon Samar da Sabon Shirin bayar da Ilimi kyauta Kuma dole da Gwamnatin jihar Kano karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta kaddamar,Kuma ta umarci Hukumar Hisbah da ta tabbatar da wannan Sabon tsari musamman ma ga Yaran da ke walagigi a kan tituna da sunan yin bara.
A cikin sumamen da Hukumar Hisbah ta kai cikin Sabongari da misalin karfe 3 na dare, an samu nasarar kamo yara masu kananan shekaru, Kuma yayin da ake bincikawa an gano cewa, a cikin Yara 68 da aka kamo wadanda suke Almajirai ne ba su fi Yara 3 ba.
A don haka ne Babban Kwamandan Hisbah Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya bayyana cewa wadannan Yara duk za a tura su Makarantun Tsangayun da Gwamnati ta Samar domin a dinga koya musu Karatun Addini da na zamani tare Kuma da kulawa da dawainiyarsu da Kuma lafiyarsu kamar yadda Gwamnati ta yi alkawari.
Ko da jin haka sai Yaran suka fara raha da murna tare da yin addu’a ga Gwamnatin Kano bisa ga wannan kulawa da za su samu.