Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari tace ‘yarta ta killace kanta bayan data dawo daga kasar Ingila, yayin da cutar coronavirus ta fara kamari a can.

A rubutun data wallafa a shafinta na Twitter, Aisha Buhari ta ce a ranar Alhamis ne ‘yar tata wacce ba ambata sunanta ba ta dawo gida Najeriya daga Birtaniya.

Ta ce yarinyar ta killace kan nata ne saboda shawarar da Ministan Lafiya na kasa ya bayar, ba wai don ta nuna alamun cutar ba.

Ta kuma yi kira ga iyaye su dauki irin wannan matakin idan yaransu sun dawo daga tafiya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *