Daga; Salisu Musa Jegus
Wutar wasannin guje guje da tsalle tsalle ta kasa ta shekara ta 2020 ta iso jihar kano , wutar da ake kaita jihohi da suka sami chanchantar shiga wasannin guje guje da tsalle tsalle da ake gudanarwa ta iso jihar kano ne da misalin 12 ;30 .
inda kai tsaye aka wuce da ita fadar gwamnatin jihar kano karkashi jagoranchin shugaban hukumar wasanni ta jihar kano Alh.Ibrahim Galadima,wanda zai damkata ga Gwamnan jihar kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje.
