A sanadiyyar halartar gasar da suka yi a karshen makon jiya a Croatia, wasu ‘yan wasa da mssu horas dasu sun kamu da kwayar cutar covid-19.
Dubban ‘yan kallo sun halarci gasar wadda ita ce ta biyo bayan wadda aka fara yi a birnin Belgrade.
Alamar farko cewa akwai matsala ta bayyan ne bayan da aka sanar cewa Novak Djokovic ba zai buga wasan karshe na Gasar Adria ba – Gasar da shi da kansa ya shirya, inda ake tafiya daga wannan yanki zuwa wancan domin taimaka wa ‘yan wasan na Tennis komawa bisa ganiyarsu gabanin kakar wasan Tennis ta duniya ta kankama.
Grigor Dimitrov na sanar da mabiyansa a shafinsa na Instagram da su yin gwajin cutar korona idan sun yi mu’amulla da shi
Sanarwar da aka yi yayin da ake gasar ta ce: “An dakatar da wasa saboda Grigor Dimitrov – zakaran Gasar US Open – ya kamu da cutar korona.”
Daga nan ne fa aka fara rububin gwajin sauran ‘yan wasa da masu horar dasu kuma an sanar da skamakon gwaje-gwajen a jiya.
Sakamakon ya tabbatar cewa dan Croatia Borna Coric ya kamu da cutar tare da wani kocin Novak Djokovic da wani kocin na daban.
Djokovic da sauran taurarun ‘yan wasan ba su daukin matakan kariya kamar na bayar da tazara ba yayin da wannan gasar ke gudana a Zadar.