Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga-Abbas Musa Sheka

Jami’an sintiri na unguwar ja’o’ji, sun kama wasu barayi uku da suka fasa shaguna, matasan dai sunyi tattaki tun daga Jahohin Zamfara da Sokoto.

Matasan dai a wannan lokaci na zaman gida suke amfani da wannan damar suna fasa shagunan jama’a, a unguwar Ja’o’ji a yankin Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Matasan sun hada da Abubakar Muhammad Sokoto da Lauwali Muhammad Sokoto sai kuma Ibrahim daga Jihar Zamfara.

Matasan sunce sun shiga Zaria sunyi satar suka taho jihar Kano daga nan ‘yan sintiri suka damkesu.

Umar Ussaini shine kwamandan vigilante na yankin Ja’o’ji kuma zonal kwamanda na Sheka, mutanen sunzo daga jahohin Sokoto da Zamfara, sun saci kudade da wayoyi a shagunan da suka fasa.

Yace zuwa yanzu sun mika su ga ofishin yansanda na sheka domin cigaba da gudanar da bincike.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *