Daga-Lamin Hassan

Wani mutum yasha dukan tsiya a wajen Jami’an ‘Yansanda na SARS a daidai kofar Nasarawa Kano.
Mutumin dai yana tsallakar da Dalibai titi a gadar kofar Nasarawa, ya tsayar da Jami’an yansanda wadan da suka fito daga motar suka hau dukan mutumin tare da bada barkonon tsohuwa, lamarin dayasa mutumin ya suma.
Lokacin da mutumin ya farfado wakilin Express radio, Lamin Hassan ya zantawa dashi yace “bai musu komai ba suka hau shi da duka har suka fitar masa da jini”