
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar da hanyar da ‘yan ƙasa za su nemi tallafi da na kusan kimanin naira miliyan 25 domin rage radadin halin da annobar cutar korona ta saka su ciki.
Iyalai da wannan annoba ta yi wa rayuwarsu illa za su iya neman tallafi amma sai suna da hujjar tabattar da hakan, a cewar sharuɗɗan da aka wallafa a shafin neman tallafin.
Masu kanana da matsakaitan sana’o’i ma na da damar neman tallafin matukar dai suna da hujjojin da za su tabbatar da cewa annobar ta durkusar da sana’o’insu.