Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne, a ranar Laraba sun kai hari garin Azir a karamar hukumar Damboa sun kashe mutum daya tare da raunata wasu da dama, rahoton Vanguard.

Yan ta’addan sun kuma sace kayan abinci da dabobi masu yawa bayan kone gidan mutanen garin.

 

Wasu mazauna garin da ke hanyarsu na tserewa sun yi magana da wakilin majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce, “A halin yanzu mun fake a Damboa ba masauki babu abinci ga kuma sanyi na harmatan.

“Yan ta’addan sun afka garin mu sunyi ta’addi da kyar muka samu muka shiga daji kafin muka tsere zuwa Damboa.”

Hakimin garin Damboa, Zanna Lawan Maina ya tabbatar da harin da aka kai wa mutanensa a hirar wayar tarho da ya yi da wakilin majiyar Legit.ng a ranar Alhamis.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *