Diyar Ministar harkokin matan Najeriya ta fada hannun ‘Yan bindiga
Daily Trust ta ce wasu ‘yan bindiga sun sace wata Baiwar Allah wanda ‘diya ce a wurin Ministar harkokin mata na Najeriya, Madam Pauline Talen.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da Dapit Karen a unguwar Rantiya Lowcost da ke garin Jos, a karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Filato.
Wani daga cikin ‘yanuwan wannan Baiwar Allah ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin.
Majiyar ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo unguwar Rantiya Lowcost ne, su ka kutsa cikin gidan wannan mata a lokacin da mutane su ke barci.
Tare da yin awon gaba da yar’ tata.
amar yadda ‘danuwan na ta ya bayyana, ‘yan bindigan sun zo ne da kimanin karfe 5:00 na safe.
Misis Dapit Karen wanda ta yi aure a Junairu ta na zaune ne tare da tsohuwarta a garin Jos, amma masu garkuwa da mutanen ba su dauki mahaifiyarta ba.