Yan bindiga sun kai farmaki kananan hukumomin Igabi da Chikun a jihar Kaduna
Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane da dama tare da kona wasu gidaje
Sai dai kuma, jami’an tsaro sun yi nasarar kashe da dama daga cikin maharan
Rahotanni na cewa wasu yan bindiga sun halaka akalla mutane 18 a wani hari da suka kai wasu yankunan jihar Kaduna.
A yayin wata sanarwar daga gwamnatin Kaduna, ta ce an kai hare-haren ne a kananan hukumomin Igabi da Chikun, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.
Maharan sun kuma sun sace mutane da dama tare da kone gidaje a kauyen Anaba da ke cikin karamar hukumar Igabi.
Hakazaika, baya ga garuwa da mutune yan bindigar sun kuma kuma saci shanu a kauyen Barinje da ke cikin karamar hukumar Chikun.
Sanarwar ta ce kuma jami’an tsaron Najeriya sun kashe yan bindiga da dama