Fitaccen Malamin addinin musuluncin a najeriya , Sheik Ahmad Gumi yayi bayanin yadda ‘yan bindiga suke sarrafa kudaden fansar da suke karba
Inda yace suna tattara kudaden ne don su siya makami mai linzami na harbo jiragen sama
A wata tattaunawa aka yi dashi ya bayyana hakan, inda yace ya kamata gwamnati ta yafe musu laifukansu
Ahmad Gumi, babban malamin addinin nan, ya ce ‘yan bindiga suna tattara kudaden da suke amsa a matsayin kudaden fansa daga hannun jama’a don siyan makami mai linzami na harbo jiragen saman.
Gumi ya samu ganawa da wasu ‘yan bindiga a dajin jihar Zamfara.
A tattaunawar da The Punch suka yi da Gumi, ya ce da yuwuwar ta’asar ‘yan bindiga ta karu idan gwamnati bata yi wani abu ba a kai.
Gumi ya ce ‘yan bindiga sun fi sojoji sanin lunguna da sakunan dake cikin dajikan, don haka za su yi amfani da wannan damar wurin cutar dasu, shiyasa ya shawarci gwamnati da ta sasanta dasu.
“Wadannan sune mutanen da suka fara fuskantar satar shanu, masu satar shanu da bindigogi sun raba su da shanunsu. Daga nan ne suka fara siyan makamai sai kuma garkuwa da mutane. Yanzu suna siyan miyagun makamai wadanda zasu iya tarwatsa jirgi. Wannan babban tashin hankali ne wanda yakamata a dakatar,” cewar Gumi.
“Idan aka yafe musu, za su ajiye makamansu. Sai aje a gina musu makarantu da asibitoci don zamansu lafiya ya tabbata.
“Indai da bindiga ne babu yadda za a yi dasu. Saboda sun fi sojojinmu sanin lunguna da sakunan dake dajin. Don haka gara a sasanta dasu.”