Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Al’umma a Ivory Coast na dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, duk da kafin zaben jam’iyyun adawa sun yi kira ga masu jefa kuri’a da su kauracewa zaben kwata-kwata.

Wannan ya biyo zargin da su ka yi wa shugaba Alassane Ouattara na saba kundin tsarin mulki, bayan da ya tsaya takara a karo na uku.

Bbc ta ruwaito cewa akalla mutun 14 suka mutu a rikicin watan Agusta, bayan furucin shugaban na cewa zai sake tsayawa zabe a karo na uku.

Jagororin adawa da suka hada da Pascal Affi N’Guessan da kuma Henri Konan Bédié sun ce kundin tsarin ulki ya haramtawa shugaban tsayawa wata takarar bayan wa’adi biyu.

A don haka su ka yanke shawarar kauracewa shiga zaben suka kuma bukaci al’umma da su nuna rashin amincewar su.

To sai dai a hira da wani dan jarida da ke can, BBC ta fahimci cewa al’umma sun fito rumfunan zabe, kuma a mafi yawan sassan kasar zaben ya gudana lami lafiya.

Yanzu haka a na kan kirga kuri’u, bayan kammala jefa kuri’a da yammacin Asabar, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Reuters ya ruwaito.

An samu rahotannin tashin hankali a yankunan da yan adawa suka fi karfi, wanda ya hada da rufe hanyoyi da kuma kona kayan zabe.

To sai dai bayan jefa kuri’arsa a birnin Abdijan, shugaba Alassane Outtara ya nemi da a daina zanga zanga.

An ambato shugaban yana cewa ‘ina kira ga wadanda su ka kira boren da ya yi sanadin rasa rayuka da su daina’.

A na saran samun sakamako zabe a cikin mako mai zuwa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *