Mai fafutukar kare hakkin bil adama Sanata Shehu Sani, ya ba hukumomin Najeriya shawara kan yadda za a magance matsalar garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ke yi akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A cewar Sanata Sani, hanya daya da za iya magance wannan matsala ita ce a dauki matasan kauyukan da ke kan hanyar a aikin dan sanda da na hukumar tsaron al’uma ta Civil Defence a kuma tura su yankunan domin su samar da tsaro.
“Akwai kauyyuka 37 akan wannan hanya. A dauki matasan wadannan kauyuka a aikin dan sanda sai a tura su aiki a wadannan kauyuka don su rika kare hanya su kuma tunkari masu garkuwa da mutanen, domin sun san yankin sosai.” Sani ya fada a shafinsa na Twitter.