Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaba Mohammadu Buhari ya taya yan Najeriya murnar samun nasarar kauda cutar shan Inna a fadin kasar bayan daukar shekaru ana yaki da cutar ba dare na rana, abin da shugaban yace abin ayaba ne tare da alfahari,

Haka nan shugaban kasa Buhari ya godewa duk wadanda suka bada gudummawa ciki da wajen kasar nan dan ganin an samu nasarar musamman maikatan lafiya maza da mata wadanda sukai aiki tukuru dan ganin hakan ya tabbata,

Mataimaki na musammam ga shugaba Muhammad kan harkokin yada labarai Malam Garba shehu ya bayyana haka ga manema labarai a wata takarda da ya fitar lahadi,

Inda yace nasarar da akasamu yar manuniyace na irin goyon baya da alumar najeriya duka bayar a kokarinsu na ganin an kakkabe cutar daga najeriya, a inda ya kara dacewa nasarar kauda cutar kamar zuba jarine ga rayuwar matasa masu zuwa nan gaba abin da zasuyi alfahari dashi, ya Kara dace bunkasa harkokin lafiya na cikin manufofin gwamnatin sa tun shekara ta 2015 lokacin da gwamnatin ta kafu

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *