Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano a arewacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu da ake zargin mahaifiyarsu da aikatawa.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya da ke kwaryar birnin Kano.

Kanin mahaifin yaran da aka kashe mai suna Sadik Haruna ya shaida wa manema labarai cewa matar ta samu sabani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya.

Yaran da ake zargin mahaifiyar tasu ta kashe su ne Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da ‘yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekara uku kuma sun gamu da ajalin nasu ne ranar Asabar.

“Tun bayan ya yi aure ta ƙi kwantar da hankalinta,” in ji Sadik. “Kuma auren nasa bai fi wata biyu ba zuwa uku.”

Ya ƙara da cewa: “Ba yanka su ta yi ba amma akwai yankan wuƙa a jikinsu da sannan kuma akwai rauni a kansu, wanda shi ne ya fi yi musu illa.

“Mijin nata ba ya gidan a lokacin da abin ya faru kuma har sai da ta kira shi suka yi waya kafin ta aikata kisan”.

Lamarin ya daure wa mutane da dama kai a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano, musamman makwabtan gidan da lamarin ya faru, inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar ba ta da tabin hankali haka kuma ba a san ta da shaye-shaye ba.

Sai dai wasu sun kuma alakanta abin da matar ta yi da karin auren da mjinta ya yi a ‘yan kwanakin baya, wanda har ta kai ga sun samu rashin jituwar da ya janyo mutuwar aurensu amma daga baya aka daidaita su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *