Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alla-wadai da kisan da ake zargin mayaƙan Boko Haram sun yi wa wasu mazauna ƙauye a jihar Borno.

A ranar Asabar ne aka samu rahotannin da ke cewa wasu da ake tunanin mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonaki inda suka kashe fiye da mutum 40.

Lamarin ya faru ne a yankin Kwashebe a Zabarmari da ke cikin ƙaramar hukumar Jere ta Borno, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar wa BBC.

Sun ce maharan sun abka wa manoman ne yayin da suke girbin shinkafa. Kuma bayanai sun ce an ɗaure manoman ne sannan aka yi masu yankan rago.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *