Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban makaratar koyar da sharia addinin musulunci ta jihar kano wato Aminu kano Legal farfesa Balarabe Jakada Majidadin Kauran Katsina ya jadda aniyar makarantarsa na tallafawa yunkurin gwamnatin jihar kano na yaki da cutar Covid 19,

A wajabin sa yayin kaddamar da Dakarun Covid 19 irinsa na farko tsakanin manyan makaratun jihar kano tun bayan da gwamnatin kano karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Jakada yace ya zama wajibi subkufa irin wancan kwamiti na dakaru a cikin makarantar sa laakari da yadda makarantar take tamkar Gari inda yace samar da Dakarun zai taimakawa yunkurin da gwamnati keyi na fadada kokarinta na dakile cutar covid a fadin jihar kano,

Da yake bayani kan ayyukan dakarun Majidadin Kaura cewa yayi aikin farko shine na wayar da kan dalibai kan illar cutar da hanyoyin kare kai,cikin lallami da siyasa tare da sanya ido dan ganin dalibai na sanya Takunkumin Baki a makarantar da tabbatar da dokar kan masu kunnen kashi, inda daga bisani ya yabawa yan kwamitin da suka zabo Dakarun wanda yace sun zaben bisa dacewa,

Da yake gabatarda Dakarun ga shugaban makarantar dan kaddamarwa shugaban kwamitin Dakarun Malam Sani Namadi yace an zabo dakarun ne daga sassa daban daban da kungiyoyi daban daban daga makarantar bisa chanchanta

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *