Shugaba kwalejin Farfesa Muktar Kurawa, “yace suna idar da sallar Azahar sai aka sanar dasu cewa wuta ta kama sasahin Economic and Cooperative na kwalejin, “babu asarar rai saidai ta bencinan zaman dalibai da takardunsu duk sun kone”
zamu kafa kwamiti da zai binciki abin daya haddasa tashin wutar kan cewa da rana tsaka ta kama misalin karfe 1:10 pm”
wasu mutane dake cikin kwalejin sun shedawa wakilinmu Nura Aliyu cewa “suna aikinsu akace dasu wuta ta kama shine suka je kai dauki kafin zuwan jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano.”
Hukumar kashe gobara ta jihar “tace babu asarar rai ko jikkata amma har zuwa yanzu basu kammala binciken abin daya haifar da tashin wutar ba a cikin kwalejin Kano Polytechnic”.
