Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni ne tauraron mawaƙi Michael Jackson ya cika shekara 11 da mutuwa bayan shekara kusan shekara 40 yana jan zarensa a fagen waƙa.

Mawaƙin ɗan Amurka ya karaɗe lungu da saƙo na duniya da waƙoƙinsa, waɗanda da ya fara tun bai balaga ba kuma da alama har duniya ta tashi ba za a manta da su ba.

Michael Jackson ya rasu ranar 25 ga watan Yunin 2009 yana da shekara 49 bayan ya sha wasu kwayoyi fiye da kima, a cewar rahotanni.

Daga cikin irin ra’ayoyin da kuka bayyana mana, mun tsakuro irin waƙoƙin da suka burge ku kuma kuke tuna shi da su.

Waƙar They Don’t Care About Us ta yi fice matuƙa tun bayan sakinta a shekarar 1995 kuma samari a ƙasar Hausa musaman waɗnda ba su ƙware a Ingilishi ba kan ba ta sunaye iri-iri.

Wani mai bibiya mai suna @bukarkundila a shafin Twitter ya ce shi waƙar da ta fi burge shi ita ce “awara da yaji da ɗumi-ɗuminta”, yana nufin “They Don’t Care About Us”.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *