Wikki Tourists ta garin Bauchi tayi fafata da Lobi Stars da ci 4-0 a wasan mako na 20 a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya da suka fafata a Bauchi ranar Lahadi.
Manu Garba ya sanya wikki gaba minti uku da fara wasa, haka kuma ya kara ta biyu na wasan.
Inda Idris Guda shima ya ci wa Wikki kwallo biyu a fafatawar da ya bai wa kungiyar maki uku da take bukata
Da wannan nasarar Wikki ta koma ta 12 a teburi da maki 25, bayan da ta buga karawa 20.
Enyimba ta doke Wikki a kwantan Firimiya
Kano Pillars ta yi wasa 13 a jere ba a doke ta ba
MFM ta taka wa Kano Pillars burki a gasar Firimiya
An kammala zangon farko a gasar Firimiyar Najeriya
Plateau United ta koma ta daya a teburin Firimiyar, bayan da ta ci Dakkata 2-0, karo na biyu kenan da Dakkata ta yi rashin nasara a wasan waje, na farko shi ne a gidan Mountain of Fire.
Kano Pillars kuwa 1-0 ta doke Mountain of Fire, wadda ta zura mata kwallo 3-0 a wasan mako na 19 ta kuma taka mata burkin buga wasa 13 a jere ba tare da an doke ta ba.
Nasarawa United ta dan yi sama zuwa mataki na 19 daga na 20, bayan da ta ci Jigawa Golden Stars 1-0.
Adamawa United ce ta koma ta karshe ta 20, bayan da Heartland ta sharara mata kwallo 5-0.
Sakamakon wasannin mako na 20 da aka buga:
Rangers 1-2 Akwa United
FC Ifeanyiubah 3-1 Sunshine Stars
Heartland 5-0 Adamawa United
Kano Pillars 1-0 MFM
Kwara Utd 1-1 Rivers United
Plateau United 2-0 Dakkada
Nasarawa United 1-0 Jigawa Golden Stars
Warri Wolves 2-0 Katsina United
Contact Information
114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano
We Are Available 24/ 7. Call Now.
- 27 September, 2023
Share: