Getty ImagesCopyright: Getty Images
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargaɗin cewa har yanzu babu alamun gushewar cutar korona.
Wani babban jami’in hukumar Mike Ryan ya bayyana ƙaruwar waɗanda ke mutuwa sakamakon cutar zuwa 50,000 a kowacce rana a matsayin abin tsoro.
Ryan ya faɗawa wani taro da aka gudanar ta bidiyo a Geneva cewa akwai jan aiki a gaba, matsawar gwamnatoci na son rage yaɗuwar cutar da kuma kare marasa galihu.
WHO ta ce yayin da yawan wanda suka kamu ya haura miliyan 30, sannan yawan waɗanda suka mutu ke riskar miliyan ɗaya, dole ne ƙasashen duniya su tashi tsaye kafin a kai ga kawo ƙarshen cutar.