Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta, WAEC, ta fitar da sakamakon jarrabawar Private ta 2021 na farko, The Punch ta ruwaito.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata, Shugaban WAEC na Nigeria, Mr Patrick Areghan, ya ce an tsara jarrabawar ne domin taimakawa wadanda ke neman shiga makarantun gaba da sakandare samun sakamakonsu a kan lokaci.
Ya ce, “Wannan jarrabawar ita ma na kasa da kasa ne. Wannan shine karo na 4 a Nigeria, an fara ne a shekarar 2018. An bullo da jarrabawar ne domin taimakawa masu neman shuga makarantun gaba da sakandare samun sakamako kan lokaci.
“Kididdigar alkalluman ya nuna cewa dalibai Dubu bakwai da dari biyu da tamanin da tara (7,289) suka rubuta jarrabawar.
“Dubu biyu da dari tara da talatin da takwas (2,938) wato kashi 40.31 cikin 100 sun samu kredit da abinda ya fi hakan a darrusa biyar (da turanci da lissafi ko akasin haka; daga cikinsu Dubu daya da dari uku da casa’in da shida (1,396) maza ne wato (47.52%) sannan Dubu daya da dari biyar da arba’in da biyu mata ne (52.48%).