Wata Agwagwa tayi sanadiyyar gayyatar wasu mutane ofishin yan sanda a kano, wannan abin ya faru a unguwar sharada dake birnin bayan da wani yaro mai
shekaru 3 ya doki wata agwagwar da tazo kafar gidansu, abin da mai agwagwar tace sam bata lamunta ba, inda ta garzaya ofishin yan sanda na sharada ta kai koke, inda ofishin ya gayyaci wadanda ake zargi.
Kakakin rundunar yan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna kiyawa ya tabbatar da faruwar alamarin inda yace zaayi bincike dan tabbatar da adalci,