Kungiyar Lafiyan Duniya (WHO) ta fifita wasu kasashen Afrika kan Najeriya wajen aika rigakafin cutar Korona Pfizer-BioNTech.
Diraktar WHO na yankin Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce an zabge Najeriya ne bisa wasu dalilai.
Daga cikin kasashen Afrika 13 da suka bukaci rigakafin, kasar Cabo Verde, Rwanda, South Africa da Tunisia aka zabi fara turawa.
A cewar Moeti, ba karamar kalubale suka fuskanta ba wajen zaben kasashen saboda rashin isasshen rigakafin.
“Muna kyautata zaton aiki da sauran kasashen domin ganin sun samu daga baya,” tace.
“Bayan haka, kimanin rigakafin Pfizer-BioNTech 320,000 aka ajiyewa kasashen Afrika hudu: Cabo Verde, Rwanda, Afrika ta kudu da Tunisiya. Za’a kai musu a watan Febrairu.”
A cewarta. kasashen Afrika 13 suka bukaci rigakafin kuma an zabi 4 ne bisa:
1. Adadin wadanda cutar Korona ta kashe a kasar
2. Sabbin wadanda suke kamuwa da cutar
3. Isasshen kayan aikin iya ajiyan rigakafin (Sanyin kasa da -70 kan ma’aunin Celcius)