Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata rana tsohon Firayim Ministan kasar Burtaniya, Winston Churchill, ya taba cewa:

-Na dauki taksi wata rana zuwa ofisoshin BBC domn na yi hira dasu, a lokacin da na isa, na nemi direban taksi ya jira ni na tsawon minti arba’in har na gama hirar, anma direban ya nemi afuwa ya ce, “Ba zan iya ba, saboda sai na koma gida don jin jawabin Winston Churchill”

Na yi matukar mamaki kuma na yi farin ciki da sha’awar da mutumin ya nuna zai saurari jawabina! Don haka sai na cire fam 20 na ba wa direban taksi ba tare da na gaya masa ko ni wane ne ba.

Lokacin da direban ya amshi kudin, sai ya ce: “Zan jira na tsawon awanni har sai kun dawo yallabai! Kuma hirar Churchill din banza.

Kuna iya ganin yadda aka canja masa ra’ayi don son kuɗi ko; an sayar da ƙasashe don kuɗi; an siyar da daraja da kuɗi; iyalai sun rabu saboda kudi; abokai sun rabu don kuɗi; akwai mutanen da aka kashe don kuɗi; kuma ana sanya mutane bayi don kuɗi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *