Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
Karfen wayar lantarki da wani matashi yau a jihar Kano

A safiyar ranar Laraba al’ummar Garin Dakatsalle dake yankin karamar hukumar Bebeji, suka wayi gari da ganin wani abin alajabi.

Inda wani matashi ya hau kan babar waya ta lantarki data kawo jihar Kano mai karfin dubu dari uku da talatin batare da kaya a jikinsa ba.

Wannan dalili yasa D.P.O garin ya isa wajen tare da lallashin matashin dan ya sakko amma yace bazai sakko ba sai an kawo motocin yansanda biyar.

Wani mazauni garin Dakatsalle mai suna Abdullahi Auta, ya shedawa wakilinmu Abubakar Sale Yakub cewa.
“Su kansu basu san daga Inda matashin yake ba.

Dan uwan matashin yace “mahaifan saurayin sun rasu kuma yana fama da larurrar tabin hankali sannnan ya fada rijiya har sau uku.

Da yake jawabi shugaban Tashar rarraba wutar lantarki na Jihar Kano, Injiniya Muhammad Kamar Bello, yace “Allah ne yayi da kwanan matashin a gaba domin wannan waya ita ce ta kawo wutar jihar Kano baki daya kuma tana da karfin dubu dari uku da Talatin.

Zuwa yanzu dai matashin ya sakko daga kan babbar wayar lantarkin, yana kuma fama da larurar tabin hankali amma an kaishi asbitin gwamnatin domin bashi kulawa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *