Wani mai suna femi mazaunin rukunin gidaje a lekki dake jihar Lagos ya kashe matar sa daga bisani ya kashe kansa,
Wasu shedun gani da ido da suka bukaci a boye sunamsu sun bayyana crwa maauratsn biyu sun dawo tukunin gidaje ne kimanin makwanni 3 da suka gabata, shedun suka kara da cewa ba kowane ya sansu suba, amma ko kafin mutuwar tasu makwanni 2 anga maauratan 2 suna gudu dan motsa jiki tare,
S ranar lahadi ne makocin mutanen yace yaji an kunna sauti Mai kara inda sautin ya dauki lokaci baa kashe ba kuma baa rage karar ba,abin daya dameshi ya kai Kara ga hikimomin gidajen Wanda sukazo Dan yiwa magidanta magana su rage karar,
Tare da kanwar matar gidan da take kasan benansu, bayan daukan lokaci suna buga kofar baa budeba sai suka yanke shawarar karya kofar, shigarsu keda wuya sai suka iske matar da mijin a mace,
Wata majiya data nemi a sakaya sunanta tace maauratan nada ya’ya’ biyu inda maigidan ke zargin matar kan dansu na biyu,
Kakakin Rundunar yan sandan jihar Lagos Bala Elkana ya tabbatar da faruwar alamarin inda yace an mika batun ga sashin bincike na LIB bayan da aka sami wukake biyu da wasu abubuwa a inda abin ya faru