Wata kara da aka shigar tsakanin wani mutum da tsohuwar masoyiyarsa a garin Yola na jihar Adamawa, ta dauki hankali bayan da mutumin ya zaro wuka ya dabawa matar a gaban kotu.
Wanda ake zargin ya nuna cewa ya fusata da hukuncin Kotun Yankin Masu Laifi na 11 dake Yola, na sauya yarjejeniyar magana da matar ta yi na biyan N85, 000 ga mutumin bayan sun goyi bayan shirin aurensu.
Enoch Adamu ya maka Ashini Hosea a kotu kan neman a biyashi kudin. Ya so a dawo masa da duk kudin da ya ce ya kashe kan Ashini wanda ya janye daga shirin aurensu. Kudin sun hada da kudin baiko.
Ashini ta amince zata dawo da N85000. Duk da haka, kotun ta soke biyan kudin a ranar Alhamis.
Hukuncin kotun bai yi wa Adamu dadi ba wanda ya dauki wuka ya dabawa tsohuwar masoyiyar tasa.
An garzaya da Ashini asibiti don yi mata magani yayin da aka kama Adamu kuma aka kulle shi a sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sanda (CID).
Duk da haka, wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin tserewa daga hannun ‘yan sanda. Ya yi tsalle daga inda aka ajiye shi domin ya sauka kasa.