Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta kubutar da wani mutum da ya yi yunkurin kashe kansa a ‘tashr mota dake Ikeja ranar Asabar.

Shugaban LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Oke-Osanyintolu ya ce, mutumin ya fado ne daga tsauni yayin da yake kokarin kashe kansa kuma an yi kiran gaggawa ga hukumar bayar da agajin gaggawar.

Ya ce, “Mun samu kiran waya ne da misalin karfe 9:50 na safe game da wani mutum da aka ruwaito ya yi yunkurin kashe kansa a ‘National Bus Stop’ da ke Ikeja. Wannan ya sa nan da nan masu aiyukan mu na gaggawa suka garzaya zuwa wurin domin aiki.”

Ya bayyana cewa, lokacin da tawagarsa suka isa wurin, sun gamu da wani babban mutum wanda ya sami rauni a diddigen kafarsa ta hagu.

Oke-Osanyintolu ya kara da cewa, wanda ya yi yunkurin kashe kan nasa ya samu raunin gocewar kashin ne bisa buguwar da ya yi sanadiyyar shan barasa wanda hakan yasa ya yi kokarin kashe kansa.

Bayanai da aka tattara a wurin da lamarin ya faru shine cewa, babban mutumin ya fado daga tsaunin ne tare da kokarin kashe kansa.

“A wurin da abin ya faru, an tabbatar da tsaro, an wanke ciwon na shi, an auna wanda shi kuma an duba muhimman kwayoyin cutar tare da BP 130 / 80mmHG, PR 92bpm, RR 22cpm, spo2 92%, GCS 15,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “an yi amfani da tukunyar iskar shaka tare da ‘Hann Cannula’ da aka kunna da wuta a 4 a kan mintoci 45, kuma an kula da zub da jinin jikinsa da 1m 75mg na ‘diclofenac’, sannan kuma an ba shi lita ta ‘Normal Saline’”

Ya ce nan take aka kai mutumin babban asibitin Ikeja, inda yake karbar magani.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *