Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani Dattijo mai suna Sha’ibu wanda akafi sani da Dan Jummai Makeri ya rasu jim kdan da idar da sallar Juma’a Masallacin Juma’a na Ja’en.

Dattijon yana da shekaru 70,ma zaunin unguwar Shekar mai Daki, kuma shedun gani da ido sun ce da kansa yazo masallacin, kuma dashi aka tayar da sallar har aka idanar inda yayi lazumi tare da kiran wanzami dan yayi masa aski idan ya kammalawa wani mutum.

Dan Jummai makeri yana zaune yana jira sai kaiwa aka ga baya motsi hakan yasa wani mutum ya tabashi nan dai ya fahimci ya rasu, inda take ya sanya Darduma wato Sallaya ya rufe fuskarsa.

Kamar yadda wasu sheadun gani da idon suka bayyana tashar Radio Express, sunce “babu alamun wata rashin lafiya tattare da dattijon, kuma tare sukayi salla dashi.

Ko da muka tambayi guda daga cikin ‘ya yan Marigayin ko zai ce wani abu akan rasuwar mahaifin nasu sai yace “ba zan iya cewa komai ba sai dai Allah ya jikansa, indan kuma kuna bukatar wata magana akwai ya yanmu zai zo”.

Sai dai daga bisani ‘Yansandan Sharada sun zo da zummar daukar gawar marigayin tare da ‘ya yansa amma wani Babban Jami’in ‘Yansandan yace “a bari a kirawo lambar jami’an hukumar NCDC dake yaki da corona dan a gwada tsohon, lamarin da baiyiwa iyalan marigayin dadi ba akaso abaiwa hammata iska.

Rahotanni sun nunar da cewa har zuwa lokacin da mukabar masallacin Juma’a na Ja’en din Jami’an NCDC basu zo ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *