Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An damke wani dan sanda mai suna Shedrack Igwe da laifin satar bindigogi

An kama Jami’in Igwe wanda ke aiki tare da rundunar ‘yan sanda na Abia a Ebonyi inda ya gudu bayan ya saci bindigogin

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi ya tabbatar da faruwar wannan al’amari

An damke Shedrack Igwe, wani jami’in dan sanda a jihar Abia da ake zargi da satar akalla bindigogi AK-47 daga sashin rundunonin ajiye makamai na MOPOL Base 28, Umuahia, inda yake aiki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Igwe wanda dan sanda ne ya saci bindigogin tare da taimakon wasu wadanda har yanzu ba’a bayyana sunayensu ba.

Legit.ng ta tattaro cewa ya saci bindigogin ne a ranar Talata, 2 ga watan Maris, sannan ya tsere zuwa jihar Ebonyi, mahaifar sa, inda daga baya hadaddiyar tawagar ‘yan sanda daga jihohin Abia da Ebonyi suka kama shi

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *