Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ishaq Usman Bello, babban alkali a babbar kotun tarayya da ke Abuja (FCT), ya rasa damar zama alkali a kotun hukunta manyan laifukan ta’addanci da cin zarafi ta kasa da kasa (ICC) da ke Geneva, Switzerland.

Hakan na kunshe ne a cikin sakamakon zaben da aka gudanar ranar Alhamis wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na kotun ICC, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A watan Yuni na shekarar 2020 ne shugaba Buhari ya zabi Jastis Bello a matsayin dan takarar Najeriya a neman kujerar alkali a kotun ICC.

A zagaye na farko da aka gudanar da zaben neman kujerar, Jastis Bello ya samu kuri’u 12 ne kacal, inda ya zama na biyu a mafi samun karancin kuri’u daga cikin jimillar kuri’u 117 da aka kada.

Da aka sake yin zaben a karo na biyu, Jastis Bello ya samu kuri’u biyar ne kacal daga cikin kuri’u 110 da aka kada.

Tun a cikin watan Oktoba kwamitin bayar da shawara ya nuna alamun ba zai kai ga nasara ba a karshe bayan sun nuna alamun bai samu karbuwa ba.

‘Yan takarar kasashen Ingila da Georgia, Korner Joanna da Lordkipanidze Gocha, aka zaba daga cikin ‘yan takara 18.

Alkalai shidda ake sa ran zaba domin cika kaso daya cikin uku na jimillar alkalai 18 da kotun keda su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *