Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga -Salisu Musa Jegus

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa ta dakatar da dukkan wasannin Zakarun Turai na Champions da Europa League saboda covid 19

Haka kuma Hukumar ta dage gasar kasashe har da wasan cike gurbin cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 wadda aka ce sai a 2021 za a gudanar.

Tun da fari ta soke dukkan wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a wasan kwallon mata da za a gudanar a 2021.

Mambobin hukumar kwallon kafar Turai 55 ne suka cimma matsaya, bayan da suka gudanar da taro a Larabar nan.

Wadan da ya kamata su buga wasannin cike gurbin shiga gasar nahiyar Turai ta 2020 sun hada da Ireland ta Arewa da Jamhuriyar Ireland da kuma Scotland.

Kungiyoyin Premier da ke Champions League sun hada da Manchester City da Chelsea, yayin da Manchester United da Wolves ke buga Europa League.

An dage dukkan wasan karshe da ya kamata a buga a watan Mayu a kofin Champions League da Europa da kuma na mata na Zakarun kungiyoyin Turan.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *