Gudun ganganci da ababen hawa abune wanda yake haifar da mummunan haddura, tare da rasa rayuka.
Shugaban tashar Rijiyar Zaki Idris Badamasi City Boy ne ya bayyana hakan yayin gudanar da bita ga Direbobin motoci a ofishin sa.
City Boy yace mafiya lokuta hadarin da ake samu yana da nasaba da gudun- ganganci, da kuma yin tsere da wasu Direbobin suke yi a lokacin da suke kan titina.
Idris Badamasi ya yi kira ga Gwamnati data mayar da hankali wajen gyaran Titinan da suka lalace da kuma wadanda aka fara aikin su ba’a kammala ba.