Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata mai garkuwa da mutane Maryam, ta ce tsohon saurayin ta da ya guje ta ta fara sacewa

Maryam bayyana yadda kawunta ya jefa ta a harkar garkuwa da mutane bayan saurayin yaki auren ta bayan tayi kokarin shawo kansa

Daga cikin kudin fansar da aka bata tayi amfani da shi wajan kama hayar gidan zama a Kano

Rundunar yan sandan Jihar Kano a ranar Laraba ta cafke wasu masu garkuwa da mutane su hudu cikin su har da mace ƴar shekara 23, Maryam Mohammed, Daily Trust ta ruwaito.

Ta shaida cewa aikin ta na farko a matsayin mai garkuwa da mutane ya fara ta kan tsohon saurayin ta wanda yaki auren ta bayan shafe shekaru suna soyayya.

Maryam Mohammed, wanda aka fi sani da Hajiya, mai shekaru 23 an kama ta a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu mutane uku yan tawagar ta a unguwar Jaba, karamar hukumar Ungogo da ke Jihar Kano, lokacin da suke tattaunawa da iyalan daya daga cikin wanda suka sace akan kudin fansa.

Ta ce kawun ta ne ya fara jefa ta a harkar, wani Hamza Dogo na kauyen Butsa, karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara, bayan sun rabu da tsohon saurayin ta.

“Kawu na, da ake kira Hamza, dan garin Butsa, karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara kuma wanda muka fara garkuwa da shi tsohon saurayi na ne wanda ya ƙi aure na duk da ƙoƙarin da na yi na shawo kansa yayin soyayyar mu.

Da muka yi garkuwa da shi, iyalan sa sun biya miliyan 5 don kwato shi, kuma an bani 800,000 daga ciki wanda nayi amfani da su wajen hayar gida a unguwar Jaba” in ji Hajiya.

An ruwaito tawagar a matsayin daya daga cikin masu sace sacen mutane a Kano da Zamfara.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano ya ce bayan sun yi bincike sun gano mijin ta wani barawon shanu ne, Sani Ismail, dan asalin Bida wanda aka kashe a ƙauyen Butsa bayan ya sato wani garken shanu.

Ta zauna a unguwaninnin Panshekara, Medile da Unguwa Uku kafin ta koma Jaba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *