Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Muhammadu Sanusi na biyu wanda ke jawabi lokacin da majalisar malaman Sunna daga Kano ta kai mashi ziyara a masaukin shi na Kaduna, ya yi bayanin dalilin kin cewa uffan game da cire shi da gwamna jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi.

Muhammadu Sanusi na biyu wanda ke ganawa da al’umma daban-daban a Kaduna bayan kwashe dogon lokaci a jahar Ikko, ya bayyana cewa, shi ne jika na farko a tarihin masarautar Kano da Allah Ya bashi sarauta. Yace “in dai an yarda cewa, Allah ba ya zalunci, to duk abinda ya same ka idan dai baka zalunci gwamnati ko ‘yan uwanka ko kuma al’umma ba, ba kuma za a iya cewa ga abinda ka yi ba, sai ka godewa Allah ”

Tsohon sarkin ya ce abinda ya sa bai yi magana ba shine sanin cewa, “daukaka ake nema, ba mulki ba.” Yace “Allah ne ke bada mulki ga wanda Ya ga dama, saboda haka idan Ya bada mulki sai a gode masa.” Tsohon sarkin ya bayyana godiya da kaunar da yace al’umar Kano ta nuna mashi, ya kuma ce ‘yana tare da su’.​

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (Hagu) Ya Na Mika Kyauta Ga Muhammed Babangida, Wanda Ya Lashe Wasan Dawakai a Karakashin Kungiyar MTN a Lokacin Gasar Lashe Kofin Hassan E. Hadeja a Kaduna a Ranar 4 ga Watan Nuwamba, 2015

Muhammadu Sanusi na biyu ya ce idan ya yi fushi sabili da an cire shi daga sarauta ya yi wa Allah butulci, saboda yana iya hana shi mulki tun da farko yana kuma iya daukar ranshi a maimakon sauke shi daga mulki. Yace kasancewa Allah Ya bar shi da rai da lafiya da kuma iyalinshi, ya isa abin godiya.

Tsohon sarkin Kanon ya kuma ce, sarauta rai ne da ita, saboda haka mutum baya wuce ranar da Allah Ya dibar mashi, amma ba domin ikon gwamnati ba. Yace a cikin shekaru dari biyu, an yi mutane dubbai amma Allah bai basu mulki ba har da mahaifinshi da yake dan Sarki. Ya bayyana cewa ya sauke hakin al’umma dake wuyansa iyaka iyawarsa a cikin shekaru shida da ya yi yana mulki. Yana mai cewa…

“Zuri’ar Dabo mutum nawa ne, a cikin mutum dubban nan cikin shekara dari biyu, ni ne na goma sha biyu kadai a cikin dubbai da Allah Ya ba. Bai ba mahaifina ba kuma dan sarki ne. Bai taba ba wani jika ba, ni Ya fara baiwa wani jika …to banda ka gode masa har ka mutu, me za ka ce wa Allah?”

A cikin jawabansu, malaman Sunnan karkashin jagorancin Sheik Adam Koki da Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, sun bayyana cewa, sarauta da matsayi da kuma dajarar kujerar Sarauta tana bin mutum ne, ba kujera ba, suka kuma bayyana cewa al’ummar jihar Kano tana matukar kaunar Muhammadu Sanusi na biyu tare da yi masa fatar alheri.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *